Shin me ake nufi da 'yanci?

Image caption Wasu na kallon 'yanci a matsayin damar fadin albarkacin baki.

BBC ta soma gabatar da rahotanni na musamman kan ma'anar 'yanci a duniyar mu ta yau.

Kama daga 'yanci daga masu leken asiri, zuwa ga 'yancin zama kai kadai, BBC na gudanar da bincike a kan

A kan barun leken asiri dai, wasu gwamnatoci ko kuma mutane na yinsa da nufin tattara bayanan sirri ba tare da sanin wanda ke rike da irin wadannan bayanan ba.

Shin leken asiri domin tabbatar da tsaro ya keta 'yancin mutum?

Amfani da leken asiri don yakar ayyukan 'yan kungiyar Jama'atu Ahlisunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko-Haram ya dace?

Mahukunta dai sun dauki matakai daban-daban da nufin murkushe 'yan kungiyar, amma har yanzu matsalar ba ta kau ba, musamman ma a shiyyar arewa-maso-gabashin kasar.

To, sai dai yayinda wasu ke ganin gazawar jami'an tsaro na leken asirin miyagu shi ke kawo cikas wajen kawo karshen hare-haren, a na su bangaren wasu jami'an tsaron na da ra'ayin cewa ita ma al'umma na da rawar da za ta taka wajen inganta tsaron ta hanyar bayar da bayanai.

'Google'

Kamfanin Google da ya yi fice ta fuskar hanyoyin sadarwa na zamani ya nemi karin bayani daga Shugaba Obama dangane da shirin takaita yadda hukumomin leken asiri na Amurka suke sa ido a kan harkokin sadarwar jama'a.

Bayan kwarmata bayanan sirri na tsaro da Edward Snowden ya yi, shugaba Obama ya bayyana cewa, za'a takaita yawan bayanai ta wayar salulu na jama'a da ake diba.

Sai dai kuma babban jami'in harkokin da suka shafi shari'a na kamfanin na Google, David Drummond ya fadawa BBC cewa, ya kamata shugaba Obama ya kara haske a kan wannan batun.

Yace " Muna tunanin ya kamata su fayyace abinda suke bukata kuma su samu takarda daga jami'an tsaro a kan irin bayanan da suke bukata".