Yarjejeniyar Samsung da Google

Hakkin mallakar hoto AP

Google da Samsung sun kulla yarjejeniyar amfani da fasahar juna domin rage "barazanar shari'a" tsakaninsu da kuma bunkasa kirkire-kirkire.

Yarjejeniyar ta shafi hakkin mallakar fasahohi da dama na kamfanonin biyu da ma wasu fasahohin da za su yi wa rajista cikin shekaru 10 masu zuwa.

Dama dai kamfanonin na aiki tare, inda Samsung ke amfani da fasahar Android ta Google a wayoyinsa na komai-da-ruwanka.

Samsung ya ce yarjejeniyar na da matukar muhimmanci ga sana'ar kere-keren fasaha kuma zai rage barazanar ganin Google da Samsung a kotu bisa rikicin hakkin mallakar fasaha.

Hakkin mallakar Fasaha

Ana kuma sa ran yarjejeniyar za ta karfafe su kan abokan kasayya irin su Apple, wanda ya kai karar neman diyyar biliyoyin daloli daga Samsung bisa zargin keta hakkin mallakar fasaha.

Samsung, wanda shi ne kamfanin wayar komai-da-ruwanka mafi girma a duniya na fuskantar tuhuma daga Apple a Amurka da Koriya ta Kudu.

Apple na zargin Samsung ya kwaikwaye tsarin wayoyinsa na iPhone ne wurin kera wayoyin Galaxy.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kamfanonin biyu sun kwashe shekaru su na rikici a fadin duniya, koda yake an shirya taron sasantawa tsakanin shugabanninsu a tsakiyar Fabrairun gobe.

Karuwar kararraki

Adadin kararrakin da aka shigar game da hakkin mallakar fasaha na karuwa a yayin da kasuwar wayoyin komai-da-ruwanka da kwamfutocin hannu ke kara bunkasa a fadin duniya.

Wata fitacciyar shari'ar ta shafi gamayyar Rockstar - wacce ta kunshi Apple, Microsoft da Sony, wadanda ke karar Google da wasu kamfanonin wayar komai-da-ruwanka guda shida dake amfani da fasahar sarrafa wayoyi ta Android.

Kamfanonin sun shigar da kararraki takwas game da hakkin mallakar fasahar wayar tafi-da-gidanka ta Google.

Haka kuma Google ya na wata shari'ar da Apple game da hakkin mallakar wasu fasahohin Motorola mallakar Google.

Domin kawo karshen wadannan rikice-rikicen ne kamfanonin fasaha ke kulla irin yarjejeniyar da Google da Samsung suka bayyana.

A bara, Samsung da Nokia sun amince da raba hakkin mallakar fasahohin juna tsawon shekaru biyar, yayin da Apple da HTC suka sanar da yarjejeniyar raba hakkin mallaka ta shekaru 10 a cikin 2012.

Manazarta su ce hakan na kara karfafa kamfanonin.