Maseko ya zama dan sama jannati

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani dan Afrika ta Kudu mai shekaru 25 na shirin zama bakar fata dan Afrika na farko da zai zama dan sama jannati. Mandla Maseko na cikin mutane 23 da su ka yi nasarar samun tikitin shiga kumbon da zai fitar da su daga duniyar da muke ciki zuwa sararin Subhana na tsahon sa'a guda a 2015. Ga bayanin da ya yi wa BBC kan yadda ya doke fiye da mutane miliyan guda wurin samun tikitin.

A talabijin na fara ganin tallan sannan na ji ana yi a rediyo. Ana bukatar in tura hotona ina tsalle daga duk inda na ke so. Sai na yi tsalle daga kan wata katanga, na sa abokina ya dauki hoton ina cikin diro wa.

An kuma yi min tambayoyi game da dalilin da ya sa nake son zuwa sararin Subhana. Na ce: "Ina son zuwa inda jifa ba ya faduwa kasa, kuma in shiga tarihi a matsayin bakin fatar Afrika ta Kudu na farko da ya zama dan sama jannati."

Daga nan sai aka yi min jarrabawa uku. Ta farko ita ce diro wa da lema daga nisan kafa 10,000. Ta biyu kuma aka sa ni cikin daki mai hajijiya, da kalubalen dauko tutoci biyar daga karkashin kafa ta zuwa saman kai na a lokacin da dakin ya ke juyawa. Ta karshe kuma sai aka samu a jirgi ya tashi sama ya yi ta wuntsilawa da mu sannan ya sauko aka bamu takardu mu amsa tambayoyi nan take a rubuce ba tare da an jira mun koma hayyacinmu ba.

Cikin mu 30 daga Afrika, ina cikin ukun da suka yi nasara. Sai aka gayyace mu jihar Florida a Amurka ranar 1 ga Disamba inda muka hadu da abokan kasayya 109 daga sassan duniya daban-dabam.

Image caption Kumbon sama jannatin da zai lula da Mandla Maseko

A nan fa aka shiga gudun yada kanin wani; inda aka ci gaba da gwaje-gwajen da suka hada da tsere a jiragen yaki, da tashi sama cikin wani jirgi da ke zuke nauyin mutane da dai sauran kalubale da dama amma duk na yi nasara.

Lokacin da aka bayyana sunana cikin wadanda za'a yi tafiyar da su sai na ji kamar a mafarki; ina ga kuwa ba zan farka ba sai na gan ni cikin kumbon sama jannati zan tafi sararin Subhana.

Zan tafi da tutar Afrika ta Kudu mai taswirar nahiyar Afrika. Zan kuma tafi da wakar PJ Powers da Ladysmith Black Mambazo wacce suke cewa: "Idan na ci, ko na fadi, ko na yi canjaras, duka dai nasara ce. Duniya ce ta hadin kai, duniya gida daya. A yayin da mu ke tashi domin cika burinmu wata sabuwar rayuwa na budewa." Wadannan kalaman su na da matukar tasiri a rayuwata.

Image caption Maseko da abokan tafiyarsa da Buzz Aldrin, wanda ya yi tattaki a duniyar wata.

'Yan uwana da abokan arziki duk su na taya ni murna. Duk in da na ratsa a Pretoria sai ka ji mutane su na ce min: "Muna tare!"

Fata na shi ne in kafa tarihi. In bude idon matasan Afrika su fahimci cewa babu abinda yafi karfinka, ko daga ina ka fito in dai ka zage damtse ka yi aiki tukuru.

Bayan na dawo daga sararin Subhana ina fatan kammala karatuna na aikin injiniya. Na dakatar da karatun ne kafin gasar saboda rashin kudi.

Zan so in zama injiniyan jiragen sama, in kware a fannin kula da kumbonan sama jannati saboda wata rana ni ma in je duniyar wata in dasa tutar Afrika ta Kudu a wurin.