An bukaci Nijar ta saki 'yan jarida

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya zartar da dokar hana kama 'yan jarida bisa aikinsu.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Nijar na neman gwamnatin kasar ta sako 'yan jaridu biyun da take tsare da su.

Kwanaki uku da suka wuce ne aka kama editan jaridan l'Enqueter, Sumana Idrisa Maiga da wakilin gidan talbijin Bonferey, Abdullahi Maman Amadu.

Ana dai tuhumar Sumana Maiga ne da laifin yunkurin juyin mulki bayan da ya yi rahoton wasu 'yan siyasa sun sha alwashin gwamnati mai ci ba za ta kai badi ba.

Shi kuma Abdullahi Amadu ya yi hira da wani dan adawa ne da ya zargi shugaban kasar Nijar da cin hanci da rashawa, abin da ya jawo aka kama shi tare da dan adawar.

Sai dai shugaban cibiyar kare hakkin 'yan jaridar Nijar, Malam Diallo Bubakar ya shaida wa BBC cewa kama 'yan jaridar keta hakki ne da ya saba wa dokokin Nijar.

Karin bayani