Majalisar Pakistan za ta gana a kan Taliban

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Zauren majalisar dokokin Pakistan a Islamabad.

Majalisar dokokin Pakistan za ta yi zaman musamman ranar Litinin domin tattauna matakin da za a dauka game da 'yan Taliban a kasar.

A bana dai, mayakan Taliban sun kashe fiye da mutane 100 a Pakistan.

Akwai sabanin ra'ayi tsakanin 'yan kasar game da tattaunawa da 'yan Taliban ko kuma yakarsu.

Wakilin BBC a Islamabad ya ce mutane da yawa sun kosa da abin da suke kallo a matsayin rashin katabus da shugabanninsu ke yi.