Babu ci gaba a taron sulhun Syria

Image caption Al'ummar Homs na tsananin bukatar agaji

Babu wani takamaiman ci gaba game da batun kai agaji zuwa birnin Homs a taron sulhunta rikicin Syria da ake yi a Geneva.

Majalisar Dinkin Duniya da 'yan adawa na matsa wa wakilan gwamnati su amince a kai agajin zuwa Homs ba wai kawai bai wa mata da yara damar fita daga birnin da gwamnatin ta alkawarta ba.

Kakakin ma'aikatar hulda da kasashen waje ta Amurka ya ce kwashe mutanen bai wadatar ba.

A garin na Homs kuma, mayakan 'yan adawa na bukatar janyewar sojojin da suka yi musu kawanya kwatakwata.

Karin bayani