Za a ci gaba da sulhunta rikicin Syria

Lkhdar Brahimi, mai shiga tsakani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai shiga tsakani a tattaunawar Sulhun Syria Lakdhar Brahimi

Bangarorin da ke rikici da juna a Syria za su ci gaba da tattaunawar da suke yi ranar Litinin a Geneva, zuwa wasu batutuwan na siyasa, musamman batun da suke takaddama kansa na karbe ikon mulki a kasar.

Sai dai kuma za a ci gaba da tattaunawar a kan wasu al'amuran da a ba a riga an yanke shawara kan su ba, kamar na bai wa ayarin masu kai kayan agaji kafar shiga yankunan da aka rutsa da wasu mutane da ke bukatar taimako a birnin Homs.

A ranar lahadi, wakilan gwamnatin Syria sun amince da wani shiri na kyale mata da yara ficewa daga birnin, to amma suka ce ana bukatar jerin sunaye na maza manya da ke son fita daga birnin.

Wasu shugabannin adawa sun nuna rashin amincewarsu da wannan, su na neman a ba su tabbacin ba za a tsare wadanda ke kokarin ficewa daga birnin na Homs ba.

Karin bayani