An kashe mutane 80 a Adamawa da Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jihohin Adamawa da Borno na karkashin dokar ta baci

Bayanai na kara fitowa fili game da harin da aka kai a wani coci a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Nigeria.

Bishop na Yola, Dami Stephen, ya shaidawa BBC cewar 'yan bindigar sun rufe kofar cocin ne dake kauyen Waga Chakawa ana gab da kamalla addu'o'i sannan suka karkashe mutane.

Rahotanni sun nuna cewar mutane 30 ne, ciki har da yara kanana, suka mutu sakamakon harin.

Sannan a wani harin da aka kai a jihar Borno, mutane kusan 50 ne suka mutu.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da kaddamar da wadannan hare-haren biyu.

Karin bayani