Ma'aikaciyar BBC Anne Waithera ta rasu

Image caption Margayiya Anne Waithera

Ma'aikaciyar BBC, Anne Waithera ta rasu sakamakon cutar daji da ta shafe shekaru biyu tana jinya.

Anne wacce ta soma aiki da bangaren rediyo na BBC a shekara ta 2009 ofishinmu dake Nairobi na kasar Kenya, ta rasu a ranar Litinin da daddare.

Ta na aiko da rahotanni ne daga birnin Addis Ababa a harshen Swahili da Ingilishi.

Ta rasu kasa da makwanni da rasuwar wani babban ma'aikacin BBC, Komla Dumor.

An yi juyayin rasuwarta, inda Editan Afrika na BBC Solomon Mugera ya bayyana margayiyar a matsayin "mai kwazo da hazaka".

Shi ma Razvan Scortea mai lura da ofisoshin BBC a kasashen waje ya ce "Na ji takaicin mutuwar. Anne ma'aikaciya ce mai sadaukar da kai".

Shugaban sashin Swahili, Ali Saleh da shugaban ofishin BBC a Nairobi, David Okwemba sun bayyana alhininsu game da rasuwar.

Anne ta mutu tana da shekaru 39.