An kama tsohon ministan shari'a na Malawi

Yaki da cin hanci da rashawa a kasar Malawi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaki da cin hanci da rashawa a kasar Malawi

An kama tsohon ministan shari'a na kasar Malawi Ralph Kasambara a bisa zarginsa da ake kan halatta kudin haram da ya yi.

Sai dai kuma ministan ya musanta zargin da ake masa na abinda ake kira badakalar Cashgate wadda yanzu haka aka kama mutane saba'in da ake zargi da hannu wajen aikatawa.

Ana dai zargin cewa an sace miliyoyin daloli daga asusun gwamnatin kasar, lamarin da ya shafi albashin ma'aikata. A makon nan ne za'a fara sauraron karar wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a wannan badakalar.

Wadannan rigingimu da ake yi da suka shafi cin hanci da rashawa a kasar suna iya kai ga tsige shugaba Joyce Banda.