Bincike kan tsare 'yan arewa 300 a Rivers

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban majalisar wakilan Nigeria, Aminu Tambuwal

Majalisar wakilan Nigeria ta gayyaci kwamishinan 'yan sandan jihar Rivers ya gurfana gabanta don yayi bayani game da tsare wasu mutane 300 'yan jihohin Jigawa da Kano.

Majalisar ta umurci Mr Joseph Mbu ya bayyana gaban kwamitinti mai kula da harkokin 'yan sanda da kuma na kare hakkin bil adama don ya amsa tambayoyi game da kama mutanen inda tace a yi bincike kan lamarin.

A karshen mako ne, rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta ce ta tsare wasu 'yan Arewa su fiye da dari uku tare da motocin bas-bas 17 bisa zarginsu da cewar su 'yan Boko Haram ne.

Sai dai bayanai sun nuna cewar mutanen wasu matasa ne wadanda suka saba zuwa ci-rani jihar ta Rivers daga arewacin kasar tun shekaru da dama da suka gabata, amma a wannan karon aka kamasu bisa zargin cewar su 'yan Boko Haram ne.

Jam'iyyar adawa ta APC ta ce matakin 'yan sandan wani yinkuri ne na jawo tashin hankali a jihar ta Rivers.

Karin bayani