Gwamnatin Rwanda na matsa wa 'yan adawa

Image caption 'Yan siyasa masu adawa da gwamnatin Rwanda na cikin matsi.

Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin Rwanda ke matsa wa 'yan adawa.

Da ya ke magana da BBC bayan ziyarar mako guda a kasar, jakadan majalisar na musamman, Maina Kiai, ya ce kusan duk wani dan siyasa da ya baiyana adawarsa na haduwa da fushin hukuma.

Ya ce an kama 'yan adawa da dama tare da tsare su bisa abinda gwamnatin ke kira yada jita-jita.

Mr Kiai ya ce ya gana da wani matashi da aka daure shekaru shida bayan da ya tattauna maganganun adawa a wani gidan giya.

Kungiyoyin kare hakkin bil'Adama na nuna damuwarsu game da barazanar da 'yan adawar Rwanda ke fuskanta.

Karin bayani