Matsalolin kananan masana'antu a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan

Masu kananan masana'antu a Nigeria sun koka game da rashin hanyar fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwannin duniya, abinda suka ce yana kawo musu nakasu wajen bunkasar tattalin arzikinsu.

Masu masana'antun na cewa tsauraran dokoki da kuma rashin samun tallafi daga gwamnati da rance daga bankuna su ne manyan matsalolin dake addabar su.

Sai dai gwamnatin ta ce ta na yin aiki da masu masana'atun dan magance matsalolin.

Korafin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar dake bunkasa futar da kaya zuwa kasuwannin kasashen waje ta shirya wani taro da masu masana'antun dan lalubo hanyar warware matsalolin a jihar Kano dake arewacin kasar.

Karin bayani