Ukraine ta halatta zanga-zanga

Tattaunawar shugaba Yanukovych da 'yan adawa a Kiev Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tattaunawar shugaba Yanukovych da 'yan adawa a Kiev

Shugaban Ukraine Viktor Yanukovych ya amince da cire dokar haramta zanga-zangar nan mai cike da kace-nace, a tattaunawa da 'yan adawa a birnin Kiev.

Kafa dokar ta haifar da tashe-tashen hankulan da aka shafe mako guda ana yi, bayan watanni biyun da aka yi zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati.

Bangarorin biyu sun kuma amince a a yiwa masu zanga-zangar da aka cafke afuwa, abisa sharadin cewa masu fafitikar zasu fice daga gine-ginen gwamnatin da suka mamaye su kuma cire shingaye.

Ministar Shari'a ta kasar Olena Lukash ta shaidawa BBC cewa an cimma yarjejeniyar.

Ta ce a bisa sakamakon ganawar, bangarorin sun amince da yarjejeniyar kada kuri'a kan dokar kasar Ukraine game da bayar da afuwa.

Ka na za a bayar da afuwar amma fa idan masu fafitikar suka fice daga gine-gine da hanyoyin da suka mamaye.

Ranar Talata ne dai ake sa ran majalisar dokokin kasar za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar da aka yi tsakanin bangarorin biyu.