Southampton ta rike Arsenal 2-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Fonte ne ya ci Arsenal kwallon farko

Jagorar Premier Arsenal ta barar da maki guda bayan da Southampton ta rike ta su ka yi kunnen doki 2-2 a filin St Mary's.

Jose Fonte na Southampton ne ya fara zura kwallo da ka.

Bayan rabin lokaci Arsenal ta farke ta kuma kara da kwallayen Olivier Giroud da Santi Cazorla.

Adam Lallana ne ya farke wa Southampton.

Golan Arsenal Wojciech Szczesny ya yi rawar gani, inda ya hana kwallayen Shaw da Fonte shiga raga.

Sai dai rashin nasarar Arsenal ta bude kofa ga Manchester City da Chelsea su sha gabanta a jagorancin teburin Premier idan su ka yi nasara a wasanninsu na ranar Laraba.