An bukaci Masar ta saki 'yan jarida

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Ma'aikatan Aljazeerah da aka kama kenan

Wasu kafafen yada labarai na duniya ciki har da BBC sun yi wani kira na hadin gwiwa da ya bukaci a gaggauta sako 'yan jaridar nan biyar dake ma'aikatan sashen Ingilishi na gidan talabijin na Al Jazeera, da ake tsare da su a Masar.

Uku daga cikinsu, da suka hada da tsohon wakilin BBC, Peter Greste, an kama su ne wata guda da ya wuce, ana kuma zarginsu da hada baki da 'yan ta'adda.

Su dai sun ce babu abin da suke yi da ya wuce tsage gaskiya kan abubuwan dake faruwa a Masar.

Su dai hukumomi a Masar sun ce za su gurfanar da 'yan jarida 20 gaban kuliya saboda wallafa labaran karya da kuma taimakawa kungiyar 'yan ta'adda.

Karin bayani