'Yar mai kudin Hong Kong ta kare madigo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gigi Chao ta auri abokiyar burminta Sean Eav a Faransa

'Yar wani mai kudi a Hong Kong da ya yi alkawarin ba da makudan kudi ga duk wanda ya aure ta ta nemi uban ya amince da cewa ita 'yar madigo ce.

Gigi Chao ta ce kamata ya yi babanta, Cecil Chao ya amince da abokiyar zamanta tare da mutantata kamar kowanne mutum.

Ms Chao, mai shekaru 33 wacce ta auri abokiyar zamanta Sean Eav a Faransa a 2012 ta kuma jaddada cewa: "Akwai mazan kwarai da yawa, kawai dai ba sabgata ba ce."

A makon jiya ne dai Mr Chao ya ce zai nunka kyautar £40 miliyan (N10 biliyan) da ya yi alkawarin bayarwa tun 2012 ga duk wanda ya auri 'yarsa.

Aure tsakanin jinsi guda dai haramun ne a Hong Kong, amma an halatta luwadi da madigo tun 1991.

Karin bayani