An kama masu haddasa husuma a Filato

Mr Jonah Jang, Gwamnan Jihar Pilato Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Mr Jonah Jang, Gwamnan Jihar Pilato

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa an kama mutane goma sha shida da ake zargi haddasa fitintinu tsakanin Fulani da yan kabilar Berom, inda mutanen dake gungu guda kan kai wa Fulani hari sus ace shanunsu kana daga bisa su kai wa Berom hari lamarin da kan haddasa rigingimu tsakanin kabilun biyu.

Jihar ta Filato dai ta dade tana fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa inda a baya-bayan nan aka samu hare-hare a kan Fulani da kuma yan Kabilar Berom musamman a kananan hukumomin Barkin Ladi da Riyom da Jos ta kudu.

Wata kungiyar 'yan banga ce dai ta ci nasarar kama mutanen tare da tallafin jami'an tsaro cikin yan kwanakin nan.

Mutanen goma sha shida da suka hada da mace guda, a cewar jagoran 'yan banga da suka kama mutanen, an kama su ne a kananan hukumomin Riyom da Barkin Ladi da Mangu dake jihar Filato wasu ma a yankin Tafawa Balewa dake cikin jihar Bauchi da kuma muggan makamai da suka hada da bindigogi da albarusai tatattre da su.

Alhaji Shehu Musa Aljan, jagoran yan bangar na kungiyar Mangar Security kuma ya bayyana wa manema labarai cewa wadanda aka kama din gungu ne da ya kunshi kabilu daban-daban wadanda kan kai wa wasu al'umomi hare-hare amma lamarin ya dauki salo na ricikin kabilanci ko na addini duk da cewa bakin bata garin guda.