An fara mahawarar kasafin kudin Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Arewa maso gabashin Nigeria na kuka da karancin kaso a kasafin kudin kasar.

A Najeriya, Majalisar Dattawan kasar ta fara muhawara a kan kasafin kudin bana, wanda aka kiyasta zai ci sama da naira tiriliyon hudu.

Sai dai tun tafiya ba ta yi nisa ba, wasu 'yan Majalisar Dattawan da suka fito daga arewa maso gabashin kasar sun fara sukar kudirin.

'Yan Majaisar Dattawan na korafi cewa gwamnatin tarayya ba ta kyauta ba dangane da tanadin da ta yi na naira biliyon biyu don habaka shiyyar sakamakon matsalar da take fama da ita a bangaren tsaro, idan aka kwatanta da abin da ta bai wa yankin Niger Delta.

A tsakiyar Disamban bara shugaba Goodluck Jonathan ya aike wa majalisun dokokin kasar kasafin kudin.

Karin bayani