Birtaniya za ta karbi tserarrun Syria

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Nick Clegg, Mataimakin Pirai ministan Birtaniya

Birtaniya ta ce za ta ba wa daruruwan 'yan gudun hijirar Syria wadanda ka iya fuskantar hadari, matsugunan wucin gadi.

Mataimakin Pirai ministan kasar Nick Clegg ya ce gwamnatin hadaka za ta bada fifiko ga matan da suke cikin hadarin yi musu fyade, da wadanda aka ci zarafinsu, da tsofaffi da kuma nakasassu.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta yi kira ga kasashen yammacin duniya da su ba da matsuguni ga 'yan gudun hijirar Syria 30,000 ta yi marhabin da wannan batu.

A baya dai gwamnatin Burtaniya ta ki amincewa da 'yan gudun hijirar, inda ta ce maimakon haka za ta bada kusan dala biliyan daya a matsayin agaji.

Karin bayani