Unesco ta koka da ingancin ilimi

Image caption Dalibai da yawa ba sa koyar komai

Hukumar bunkasa ilimi ta majalisar dinkin duniya (Unesco) ta ce rashin ingancin koyarwa a kasashe da dama ya sa yara ba sa koyar komai.

Rahoton da hukumar ta fitar ya ce kusan yara miliyan 250 ba su iya karatu da rubutu ba saboda malamansa ba su kware a koyarwa ba.

A kusan daya cikin ukun kasashen duniya, fiye da rubu'in malamai ba su da takardar shaidar koyarwa.