An sake kama Justin Bieber

Justin Bieber Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba wannan ne karon farko da ake kama fitacccen matashin mawakin ba, ko watan Disambar shekarar da ta gabata ma an kama shi da laifin cin zarafin wani direban mota.

An sake kama fitattacen mawakin nan da tauraronsa ke hasakawa dan asalin Canada Justin Bieber a karo na biyu cikin mako guda.

Tuhuma ta baya da ake wa mawakin ta shafi laifin cin zarafin wani direban Limozin a birnin Toronto a watan Disambar bara.

Ya kai kansa ofishin 'yan sanda inda daruruwan masoyansa suka je gaida shi tare da daukar hotuna.

A wata tuhumar ta daban kuma a jihar Florida, Justin Bieber ya musanta zargin tuka mota cikin maye tare da kin amincewa a kama shi.

A ranar Alhamis din makon jiya ne aka kama shi a birnin Miami yana falfala gudu da motarsa a titunan cikin unguwa wanda hakan ya saba wa dokar Amurka.

Ya kuma shaida wa 'yan sanda cewa ya sha barasa da tabar wiwi da kuma wasu kwayoyin magani.