Cocin Anglican ya soki hana auren jinsi

Hakkin mallakar hoto xxx
Image caption Archbishop na Canterbury, Justin Welby

Jagoran cocin Anglican, Archbishop na Canterbury ya rubuta wasika tare da Archbishop na York zuwa ga shugabannin kasashen Nigeria da Uganda in da su ka soki dokokin da ke hukunta masu luwadi da madigo.

Nigeria ta zartar da dokar da ta haramta aure tsakanin jinsi guda da kuma bayyana soyayya tsakanin mutane masu jini guda.

A Uganda kuma, majalisar dokoki ta kara tsananin hukuncin da za a yi wa masu luwadi da madigo ko kuma wadanda su ka san wasu su na yi amma ba su kai karar su ba.

Wasikar dai na zuwa ne daidai lokacin da Archbishop din na Canterbury ke fara wata ziyarar kwanaki biyar ga shugabannin cocin Anglican na kasashe biyar da ke yankin tsakiyar Afrika.

Batun luwadi da madigo dai ya raba kan mabiya cocin Anglican inda jagororinsa a kasashen Afrika su ka tabbatar da haramcin wadannan dabi'u yayin da jagororin kasashen Turai ke cewa lokaci ya yi da za a halatta.

Karin bayani