An kai hari a garin Giade na Bauchi

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption An kwana biyu ba a kai hari a jihar Bauchi ba

Rahotanni daga jihar Bauchi a arewacin Nigeria sun nuna cewar wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun kai hari kan wani caji ofis dake garin Giade inda suka yi kaca-kace da shi ta amfani da abubuwa masu fashewa.

A ranar Laraba da daddare ne maharan su ka dirarwa caji ofis na 'yan sandan dake garin Giade inda suka bude wuta tare da jefa abubuwa masu fashewa abin da ya yi sanadiyar konewar caji ofis din kurmus bayan musayar wuta da jami'an tsaro.

Wasu majiyoyi sun kuma shaidawa BBC cewa ko baya ga dagargaza caji ofis na 'yan-sandan, 'yan bindigar sun kuma jikkata wani jami'in dan sanda da yanzu haka ke karbar magani a asibiti, amma babu hasarar rai sanadiyar harin wanda kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wa.

Kakakin rundunar 'yan-sanan jihar ta Bauchi, DSP Haruna Muhammad, ya musanta batun cewa maharan sun dauki motar 'yan sanda, kana ya ce mutum guda ne maharan suka kubutar daga caji ofis din, yana mai cewa ga alama barayin shanu ne suka kai harin.

Jihar ta Bauchi dai na daya daga cikin jihohi da kan fuskanci hare-hare daga lokaci zuwa lokaci musamman a kan jami'an tsaro da cibiyoyinsu kuma harin na garin Giade na zuwa ne yayin da ake ganin kamar hare-hare na dada sauki a jihar idan aka kwatanta da wasu jihohi makotanta dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Karin bayani