Boko Haram: Ya kamata a kafa sansani

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane da dama sun rasa matsugunansu

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa-maso-gabashin Najeriya na nuna cewa al'ummomin da rikicin da ake yi da 'yan kugiyar boko-haram ya daidaita na fuskantar kalubale na rashin isasshen matsuguni.

Bayanai dai na nuna cewa mutanen masu yawa ne suka fice daga kauyukansu sakamakon rikicin.

A kan haka ne majalisar dattawan Najeriya ne daga jihar Borno Senata Ahmad Zanna ya bukaci gwamnati ta yi musu tanadin sansani a maimakon dora dawainiya a kan al'ummomin da ke kauyukan da suke makwabtaka da su.

Daruruwan mutane ne suka rasu sakamakon rikicin 'yan Boko Haram musamman a jihohin Borno da Yobe.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa a kokarin kawo karshen tashin hankali a yankin arewa maso gabas amma har yanzu lamarin babu dadi.

Karin bayani