Shehu Jibril "Golobo" ya rasu

Image caption Marigayi Shehu Jibril (Golobo) a cikin shirin fim.

Allah ya yi wa fitaccen dan wasan barkwanci a fina-finan Hausa, Alhaji Shehu Jibrin (Golobo) rasuwa da safiyar Alhamis.

Marigayi Golobo ya yi fice a wasannin barkwanci na dandali da gidajen talabijin kafin ya zama tauraron fina-finan Hausa.

Bayan sallar Azahar ne kuma aka yi jana'izarsa a garinsu, Talatar Mafara da ke jihar Zamfara, Nigeria.