Nijeriya: An fitar da tsarin taron ƙasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Goodluck Jonathan, shugaban Nigeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da tsare tsaren yadda za'a gudanar da taron kasa don tattauna matsololin da suka addabi Najeriyar.

A wani taron manema labarai sakataren gwamnatin kasar, Pius Anyim ya kira yau a Abuja, ya ce za a zaɓo wakilai 492 da zasu halarci taron.

Taron dai zai samu wakilai da dama da suka haɗa da na addinai, ƙungiyoyin ƙwadago, masu naƙasa da kuma dattawa.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya ce, ana son kammala taron kafin zaɓen da za a yi baɗi.

Za a kwashe watanni uku ne ana taron da ake sa ran zai duba manyan matsalolin dake addabar Nijeriya.