PDP na kara samun rauni a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo na tallata PDP

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria na kara samun rauni, sakamakon ficewar wasu daga cikin manyan 'ya'yanta zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Hakan dai na kara nuna rashin farin jinin jam'iyyar karkashin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan a daidai lokacin da ake dosar zabukan shekara ta 2015 musamman a yankin arewacin kasar.

A ranar Laraba wasu sanatocin PDP 11 su ka koma APC ciki har da tsofaffin gwamnoni uku wato Bukola Saraki na Kwara da Abdullahi Adamu na Nassarawa da kuma Danjuma Goje na Gombe.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cif Olusegun Obasanjo ya ce a yanzu batun PDP a kai kasuwa

Hakan na zuwa ne bayan da a bara wasu gwamnoni biyar su ka juyawa PDP baya su ka rungumi APC wato Rabiu Kwankwaso na Kano, Murtala Nyako na Adamawa, Abdullahi Ahmed na Kwara, Aliyu Wammako na Sokoto da kuma Rotimi Ameachi na jihar Rivers.

A cikin watan Disambar bara dai, 'yan majalisar wakilai 37 ne su ka fice daga PDP zuwa APC.

'Dinke Baraka'

A wata alama da ke nuna cewar jam'iyyar na fuskantar kalubale mafi girma tun kafa ta, tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya dakatar da duk wata hulda da jam'iyyar, bayan ya rubuta wata budaddiyar wasika ga shugaba Jonathan inda ya caccaki salon mulkin shugaban.

Hakkin mallakar hoto muazu facebook
Image caption Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu na kokarin sasanta 'ya'yan jam'iyyar PDP

Sai dai tun bayan da aka nada tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ya soma yunkurin dinke barakar da ta fara nakasa jam'iyyar.

Adamu Mu'azu ya tattauna da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP irinsu tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo da wasu sanatoci da kuma 'yan majalisar wakilai don shawo kan matsalolin da suka addabi jam'iyyar.

Ita ma PDP ta dan samu tagomashi saboda tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa sun fice daga jam'iyyar adawa ta APC zuwa jam'iyyar PDP mai mulki.

Masu sharhi na kallon danbarwar da ake ciki a PDP a matsayin wani abu da zai iya kawo mata nakasu a zabukan 2015 dake tafe.

Haka zalika, wasu na ganin cewar batun ko Shugaba Jonathan zai yi takarar shugaban kasa a 2015 ko kuma a'a shi ne abin da zai fayyace makomar jam'iyyar a nan gaba.

Karin bayani