Shugaban Ukraine ya dauki hutun rashin lafiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Ukraine Viktor Yanukovych

Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych, ya dauki hutun rashin lafiya a dai-dai lokacin da ake cikin tsakiyar rikicin da ya mamaye kasar sa.

Wata majiya daga ofishin sa ta ce shugaban na fama da matsalar numfashin sannan kuma hawan jini.

Har yanzu masu zanga-zangar kin jinin gwamnati na ci gaba da mamaye gine-ginen gwamnati tare kafa shingaye a tsakiyar birnin Kiev, tun bayan da 'yan adawa suka yi watsi da sabuwar dokar da za ta ba su 'yanci.

Zanga-zangar neman shugaba Yanukovych ya yi murabus tare da gudanar da sabon zabe na ci gaba da gudana har yanzu a kasar.

Karin bayani