An nemi hukuncin kisa ga maharin Boston

Hakkin mallakar hoto b
Image caption An nemi hukuncin kisa ga wanda ya kai harin Boston

Babban mai shigar da kara Eric Holder ya ce zai bukaci a yanke hukuncin kisa ga wanda ya rage a raye da ake zargi da hannu wajen dasa bam a garin Boston matukar aka same shi da laifi.

Ana zargin Johart Sanayef da laifin dasa bam a wajen gasar gudun yada kanin wani a watan Aprilun bara, da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane uku tare da jikkata wasu 250.

Magajin garin Boston Martin Walsh, ya ce ya na goyon bayan matakin da Mr Holder ya dauka duk da cewa bai amince da hukuncin kisan ba.

Martin Walsh, ya ce ya na jimami da addu'a ga iyalan wadanda suka rasu.

Karin bayani