Lauyoyin Knox za su daukaka kara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mai yiwuwa a nemi Amurka ta tusa keyar Knox zuwa Italy

Lauyoyin 'yar Amurka Amanda Knox da tsohon saurayinta Rafaele Sollecito sun ce za su daukaka kara kan hukuncin da wata kotun Italy ta yanke na tabbatar musu da lafin kisan wata daliba 'yar Birtaniya, Meredith Kercher, a 2007.

An yanke wa Miss Knox daurin shekaru 28 da watanni shida yayin da aka yanke wa Mr Sollecito daurin shekaru 25.

Sai dai lauyan iyalan Kercher ya ce sun gamsu da hukuncin da ake yanke.

Miss Knox, wacce ba ta halarci zaman kotun ba, ta bada sanarwa daga Seattle a Amurka cewa ta ji takaicin hukuncin kuma ba ta yi zaton haka ba.

Karin bayani