An fara takunkumin huduba a Masar

Image caption Masallacin al-Azhar na Cairo

Masallatan Juma'a da dama a Masar sun gabatar da huduba kan maudu'i guda da gwamnati ta zaba musu a karkashin wani sabon tsarin yi wa limamai takunkumi.

Maudu'in na yau shi ne muhimmancin inganta unguwannin talakawa da kuma taimakawa mabukata.

Mahukuntan Masar na ganin wannan matakin ya zama wajibi domin hana limamai tayar da kurar siyasa.

'Yan adawa sun ce an fito da tsarin ne domin dakile limaman da ke sukar gwamnatin da soji ke mara wa baya, bayan hambarar da zababbiyar gwamnatin masu kishin Islama karkashin Muhammad Morsi a bara.

Karin bayani