"A kafa hukumar cinikin dabbobi a Nigeria"

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana sato shanu daga arewa don sayarwa a kudu.

Kungiyoyin Fulani da masu sayan dabbobi a Nigeria sun nemi a kafa wata hukumar tantance sayar da dabbobi a kasar.

Kungiyoyin sun bayyana hakan ne a sakamakon yadda su ka ce ake shigo da dabbobin sata daga arewa zuwa babbar mayankar dabbobi ta kasa da ke a Agege a Lagos.

Daukar wannan mataki dai ya zo bayan kwamitin kasuwar mayankar dabbobin ta kama motar titiri cike da shanun da ta ce na sata ne daga arewacin kasar.