Taron sulhun Syria bai yi nasara ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lakhdar Brahimi na sa ran samun ci gaba a zama na biyu.

Ranar Juma'a za a kammala zagaye na farko na tattaunawar sulhunta rikicin Syria a Geneva ba tare da cimma wata nasara ba.

Gwamnatin Syria da 'yan adawa dai sun kasa daidaitawa game da tsagaita wuta, raba madafan iko da kuma ba da damar kai tallafi ga yankunan da sojoji su ka yi wa kawanya.

Sai dai mai shiga tsakani na majalisar dinkin duniya da ke shugabantar taron ya ce ya na fatan samun ci gaba a zagaye na biyu na tattaunawar da za a gudanar nan da kwanaki 10 masu zuwa.

Lakhdar Brahimi ya ce hutun zai bai wa bangarorin biyu damar nemo mafita kuma zai bai wa masu mara musu baya - musamman Amurka da Rasha - isasshen lokacin da za su daidaita matsayarsu.

Karin bayani