Ana zanga-zangar hana zabe a Thailand

Image caption Masu zanga-zangar sun kewaye gine-ginen gwamnati.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Thailand sun fara shinge gine-ginen gwamnati a kokarin dakile zaben gama-garin da za a gudanar ranar Lahadi.

Mutane sun kewaye ofisoshi a Bangkok da kuma kudancin Thailand a kokarin hana kai takardun kada kuri'a zuwa rumfunan zabe.

Masu zanga-zangar na adawa da zaben ne saboda su na son a fara gyara tsarin siyasar kasar tukuna.

Alamu dai sun nuna jam'iyyar da ke mulki ce za ta ci zaben kuma idan masu kada kuri'ar su ka fito da yawa za ta ce ta na da amincewar jama'a duk da kauracewa zaben da 'yan adawa su ka yi.