An samu 'yar maslaha a Sudan ta Kudu

Wadanda rikicin Sudan ta Kudu ya shafa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadanda rikicin Sudan ta Kudu ya shafa

Yanzu dai an kawar da daya daga cikin manyan abubuwan dake kawo cikas ga tattaunawar zaman lafiya dangane da rikicin Sudan ta Kudu.

Gwamnati ta bar wasu manyan 'yan siyasa bakwai su je wurin tattaunawar a Ethiopia.

Tun farko dai kama mutanen ne a farkon rikicin, kana aka tsare su bisa zargin yunkurin yin juyin mulki.

Amma daga bisani aka sake su kana aka mika su ga Kenya bisa wasu sharudda.