Google zai warware takaddamarsa da Turai

Tambarin Kamfanin Google Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tambarin Kamfanin Google

Tarayyar Turai ta ce ta na kyautata zaton tana dab da warware wata doguwar takaddama da kampanin matambayi baya- bata mafi girma a duniya wato Google.

Hukumar Tarayyar Turan ta shafe sama da shekaru uku, ta na gudanar da bincike kan Google, game da zargin cewa ya na amfani da matsayinsa wajen yin abubuwan da ba su dace ba a Turai. Babban jami'in tarayyar Turai mai kula da gogayya tsakanin kampanoni,Joaquin Almunia, ya ce, ya yi amanna cewa, sabbin shawarwarin da Google ya mika, cewa zai bada kafar zuwa sauran manyan shafukan matambayi baya-bata uku dake gogayya da shi, daga shafin nasa, ya magance korafin da hukumar take da shi.