Jagoran masu zanga zanga a Ukrain na asibiti

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An jikkata jagoran masu zanga-zanga a Ukrain

Gidan talabijin din kasar Ukraine ya ce a yanzu 'yan sanda masu gudanar da bincike sun bar asibitin da shugaban masu zanga-zanga Dimitro Bulatov ke kwance ana masa magani a babban birnin kasar Kiev ba tare da sun samu damar yi masa tambayoyi ba.

Mr Bulatov da yake cikin tsananin ciwo yace ya samu munanan raunuka a lokacin da aka sace shi tare da gallaza masa.

An dai ci gaba da girke jami'an 'yan sanda a kofar asibitin, sai dai ma'aikatan lafiya sun toshe duk wata kafa da za su samu isa inda Mr Bulatov yake.

Ana dai zarginsa da laifin shirya zanga-zanga, tuni kuma aka aike masa da sammaci.

Karin bayani