Za a sake zaman shari'ar Morsi

Tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Morsi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Har yanzu Mr Morsi na bai amince an hanbarar da gwamnatinsa ba, dan ya na kiran kansa halattaccen shugaban kasar Masar.

Nan gaba a yau ne za a ci gaba da daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Morsi a birnin Alkhahira.

Ana zargin Mr Morsi da mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi 14 da laifin tunzura kisan masu zanga-zanga a wajen fadar shugaban kasa a shekarar 2012.

A zaman da kotu ta yi kwanaki hudu da suka gabata Mr Morsi ya yi ta ihu a kotun yana fadar cewa har yanzu shi ne halattaccen shugaban Masar.

An dai hambarar da gwamnatinsa a watan Yulin shekarar da ta gabata bayan gagarumin gangamin da aka yi a kasar na bukatar ya yi murabus.

A jiya juma'a 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga daruruwan magoya bayan Mr Morsi a biranen Alkhahira da Al-askandariyya da kuma Fanyoum.