Atiku Abubakar ya koma APC

Alhaji Atiku Abubakar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya sanar da sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

A wata sanarwa da ya fitar, Atiku Abubakar ya ce ya yanke shawarar sauya sheka ne bayan tattaunawa sosai da magoya bayansa game da tayin da shugabannin APC suka yi masa na shiga jam'iyyar.

Atiku Abubakar ya kuma bukaci magoya bayansa da su gaggauta yin rijistar shiga jam'iyyar APC da zarar an fara don ceto Najeriyar daga halin da ta fada a ciki.

Ya bayyana takaicinsa game da rikicin daya dabaibaye jam'iyyar PDP da suka kafa, inda ya ce hakan ya sa shi da wasu jiga-jiganta suka fice daga babban taron jam'iyyar da aka gudanar a Abuja a shekarar daga gabata.