'Yan adawa sun kawo cikas a zaben Thailand

Hakkin mallakar hoto n

Masu zanga zangar adawa da gwamnati sun kawo wa zabe cikas a wasu mazabu a Bangkok babban birnin Thailand da kuma wasu wurare a kudancin kasar.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ce zabe na gudana lami lafiya a kashi 89 cikin dari na mazabun kasar. 'Yan adawa sun zargi gwamnati da tafka magudi da kuma saye kuri'un dimbin talakawan kasar.

Babbar jamiyyar adawa ta kauracewa zaben.

Ana sa ran cewa jam'iyyar dake kan mulki ce za ta sake lashe zaben.

Piraminista Yingluck Shinawatra ta ce zaben ya nuna cewa jama'ar Thailand na son dimukradiyya ta dore.

Ta kuma ce ta hanyar yin zabe ne kawai za a warware rikicin kasar.

To amma 'yan adawar sun ce zaben ba zai yi tasiri ba.

Zaben dai ya biyo bayan watanni ne da aka yi ana tashin hankali a kasar saboda 'yan adawa sun nace akan sai dai a kafa wata gwamnatin wucin-gadi da za ta maye gurbin gwamnati mai ci.

Ana dai dauki tsauraran mataka tsaro a dukkan fadin kasar, yayinda wasu sassa ma ke karkashin dokar ta-baci.

Hukumomi sunce an baza kimanin jami'an tsaro dubu 130 a cikin kasar, dubu 12 daga cikinsu kuma an jibge su ne a birnin Bangkok.

Masu sharhi dai na ganin cewa zaben ba zai kawo karshen rikicin da ya addabi kasar ba.

Karin bayani