'Zabe ya yi tasiri a Thailand'

Hakkin mallakar hoto AFP

Firaministan Thailand Yinluck Shinawatra ta ce fitowar da jama'ar kasar suka yi don kada kuri'a ya nuna cewa suna so tsarin dimukradiyya ya dore a kasar.

Babbar jami'yyar adawar kasar dai ta kaurarewa zaben, magoya bayanta kuma sun hana gudanar da shi a wasu mazabu na Bangkok da wasu sassan kudancin kasar, inda suke da karfi sosai.

To amma a hirar da tayi da BBC, Firaminista Shinawatran ta ce: "Akalla dai Ina tsammanin cewa wannan zaben yana da tasiri sosai, mutane sun fito kada kuri'a don tabbatar da yancinsu na dimukradiyya.

"Saboda haka Ina ganin cewa wannan yana da amfani, domin har yanzu mutane na ganin cewa zabe shine tafarki mafi kyau na tabbatar da dimukradiyya".

Duk da hana gudanar da zaben da 'yan adawa suka yi a wasu wurare dai, magoya bayan gwamnati na ganin cewa zaben ya yi nasara.

To amma 'yan adawa sunce zaben ba zai yi tasiri ba.

An dai dauki tsauraran matakan tsaro a dukkan fadin kasar, indda wasu sassa ma ke karkashin dokar ta-baci.

Hukumomi sunce an baza kimanin jami'an tsaro dubu 130 a cikin kasar -- dubu 12 daga cikinsu kuma a jibge su ne a birnin Bangkok.

Zaben dai ya biyo bayan watanni ne da aka yi ana tashin hankali a kasar saboda 'yan adawa sun nace akan sai dai a kafa wata gwamnatin wucin-gadi da za ta maye gurbin gwamnati mai ci.

Karin bayani