CAR: 'An kashe Krisita 75'

Hakkin mallakar hoto AP

Wani limamin coci a jamhuriyar tsakiyar Afrika ya ce a cikin mako gudan da ya wuce, an kashe Kiristoci akalla saba'in da biyar a rikicin addinin da ake yi, a garin Boda.

Ya ce wasu Musulmi ne dauke da makamai suka kafa shingaye a kofar shiga garin da kuma hanyoyin fita daga cikinsa kafin su fara kai hari kan Kiristoci.

Fada Cassien Kamatari yace, sai da ya nemi ɗauki daga dakarun faransa da kuma na kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afurka wato AU.

Ya kuma ce, mutane dubu da dari biyar ne suka nemi mafaka a cocin garin na Boda.

Faɗa dai ya sake barkewa ne cikin makon jiya yayin da dakarun sa kai na kungiyar Seleka suka soma tserewa zuwa arewacin kasar.