CAR: Fada ya ce an kashe kiristo 75

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar riko, Catherine Samba Panza ta yi alkawarin maidoda zaman lafiya.

Wani fada a jamhuriyar tsakiyar Afrika ya ce a cikin mako gudan da ya wuce, an kashe Kiristoci akalla saba'in da biyar a rikicin addinin da ake yi, a garin Boda.

Ya ce wasu Musulmi ne dauke da makamai suka kafa shingaye a kofar shiga garin da kuma hanyoyin fita daga cikinsa kafin su fara kai hari kan Kiristoci.

Fadan wanda ya bada mafaka ga mutane sama da dubu daya a cocinsa, ya ce bai san adadin musulmin da aka kashe ba, domin ana binne gawarwakin musulmin ne ba tare da bata lokaci ba.

Dubban jama'a ne aka kashe a rikicin addinin wanda ya barke bayan wani juyin mulki bara.

Karin bayani