Kawancen 'yan adawar Afrika Kudu ya rushe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dr Mamphela Ramphele

Yarjejeniyar kulla kawance tsakanin manyan jam'iyyun adawan kasar Afrika ta Kudu ta rushe, a kokarinsu na kalubalantar jam'iyyar ANC mai mulki.

Lokacin da aka kulla kawancen a makon da ya gabata, an tsayar da shugabar jam'iyyar Agang, Dr Mamphela Ramphele a matsayin 'yan takarar shugabancin kasar.

Amma kuma kakakin jam'iyyar Democratic Alliance, Mmusi Maimane ya ce Dr Ramphele ta ki cika alkawari a kan yarjejeniyar da suka kulla.

Ita dai da Dr Ramphele ta ce ta yi gaggawar shiga cikin kawancen kuma a cewarta 'lokaci ba yi ba'.

Karin bayani