Ukraine- Shugaba Yanukovych zai koma aiki

Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych

Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych zai koma bakin aiki, bayan kwanaki hudun da ya shafe yana hutun jinyar fama da cutar numfashi.

A ranar Lahadi ne dai dubannin masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin suka hallara a Kiev babban birnin kasar, yayin da yanzu haka jagoran 'yan adawar kasar Dmytro Bulatov wanda ya ce an sace shi tare da gana masa azaba a lokacin zanga-zangar ke jinya a wani asibiti dake Vilnus, babban birnin Lithuania.

A cikin makon da gabata ne aka nuna Mr Dmytro Bulatov a gidan talabijin jina-jina., bayan da Gwamnatin Ukraine ta zarge shi da shirya gagarumar zanga-zanga a kasar inda ta bada umarnin a tsare shi.

Wani jagoran masu 'yan adawa Petro Poroshenko ya ce yanzu akwai yiwuwar gudanar da bincike game da yiwa Mr Bulatov magani.

A jiya Lahadi ne dai dubannin masu zanga-zangar suka sake hallara a tsakiyar Kiev babban birin kasar suna neman da shugaba Viktor Yanukovych ya yi murabus.