Facebook ya cika shekaru 10 da kafuwa

A ranar Talata ne shafin Facebook ke cika shekaru 10 da kafuwa; sai dai wasu na hasashen cewa tauraruwarsa za ta fara dusashewa.

Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Yawancin matasan da ke amfani da Facebook sun kwatanta shi da cuta mai yaduwa

Idan dai har hasashen wani bincike da aka gudanar kwanan baya ya tabbata, to lallai za a iya cewa kasuwar Facebook na fuskantar barazana. Rahotanni da dama sun nuna cewa akasarin masu amfani da shafin -- matasa -- sun kosa da yadda shafin yake.

Wani bincike ma ya kwatanta Facebook da cututtuka masu yaduwa.

Kafafen watsa labarai na duniya dai sun wallafa irin wadannan rahotanni, yawanci tare da hoton mutumin da ya mallaki Facebook, Mark Zuckerberg, ya sha mur.

Image caption Wani rahoto ya nuna cewa an samu karuwar kashi 80 cikin 100 na mutane masu shekaru 55 zuwa sama da ke amfani da shafin

A lokacin da masu bincike daga jami'ar Princeton suka yi amfani da shafin matambayi-ba-ya-bata na Google inda suka yi hasashen cewa Facebook zai rasa kashi 80 cikin 100 na masu amfani da shi nan da shekaru uku masu zuwa, shafin ya mayar da martani mai zafi.

Kodayake wani rahoto ya nuna cewa kashi 25 cikin matasa da ke amfani da Facebook sun daina amfani da shi, amma wani binciken ya nuna karuwar kashi 80 na mutanen da ke da shekaru 55 zuwa sama suna amfani da shi.

Don haka hasashen da ake yi cewa Facebook zai rasa kaso mai yawa na masu amfani da shi ba zai razana Mark Zuckerberg ba, musamman saboda kudin shigar shafin na karuwa.

A yanzu dai shafin na Facebook, wanda aka fara a Jami'ar Harvard da ke Amurka, yana da mutane biliyan 1.23 da ke amfani da shi.

Image caption Kudin shigar kamfanin ya haura da 55% zuwa $7.87bn a 2013, sannan ribarsa ta nunka sau bakwai, lamarin da ya sa a yanzu yake da famĀ£1.5bn.

Ko ma dai me zai faru da Facebook, abin da ya fito fili shi ne: shafin ya zama kundin adana tarihin al'uma.

Karin bayani