Muhawara kan dokar rabon gado a kasar Ghana

Accra bababn birnin kasar Ghana
Image caption Accra bababn birnin kasar Ghana

Majalisar Dokokin Ghana za ta zartar da doka kan tsarin bai-daya na rabon gado, ba tare da la'akari da addini ko al'adun wata al'umma ba.

To sai dai al'ummar musulmin kasar sun nuna rashin jin dadin su saboda yadda suka ce hakan ya saba ma 'yancinsu na rabon gado kamar yadda addininsu ya tsara.

Tuni dai shugabannin addinin Islama suka fara gudanar da tarurrukan bita kan martanin da zasu mayar wa da Majalisar Dokokin kasar.

Wa'adin nan da rana 14 ga wannan watan ne Majalisar Dokokin ta ba duk wanda ke da magana game da kudirin da ya gabatar mata da shi kafin ta yi dokar.