Taron hada kan kasa bata lokaci ne - Kukah

Hakkin mallakar hoto kukahfacebook
Image caption Bishop Hassan Kukah ya ce za a bata lokaci ne kawai

Wani fitacen limamin Kirista a Nigeria ya yi fatali da batun gudanar da taron tattauna makomar kasar da shugaba Goodluck Jonathan ya shirya za a yi a bana a matsayin wani dandali na cece-kucen siyasa kawai.

Bishop Mathew Hassan Kukah wanda ya taba zama sakataren taron tattauna makomar siyasar kasar na shekara ta 2005, ya ce babu daya daga cikin matsalolin da talakkawan kasar ke fuskanta da wannan taron zai warwarewa.

Bishop Kukah ya kara da cewar "Ba taro bane da zai warware matsalar kasar, 'yan siyasa za su gayyaci 'yan koransu don halartar taron, daga karshe ba za a cimma wata manufa ba".

"Taron kasa ba zai warware matsalar lantarki da yunwa da abubuwan da suka addabi 'yan Nigeria ba", in ji Kukah.

Tuni jam'iyyar adawa ta APC ta bayyana cewar taron zai zama tamkar bata lokaci ne.

Karin bayani