Cutar kwalara ta kashe mutane 30 a Benue

Cutar amai da gudawa a Najeriya
Image caption Cutar amai da gudawa a Najeriya

A Najeriya an samu bullar cutar amai da gudawa wato garin Makurdi jihar Benue da ta haddasa asarar rayukan mutane akalla talatin.

Cikin wadanda suka mutun har da yara da kuma iyaye masu shayarwa, a yayinda wasu mutanen kuma ke kwance a asibitoci don karbar magani.

Cutar ta amai da gudawa ta fara bulla ne tun daga ranar Asabar din da ta gabata a unguwannin Wadata 'Yan rake da kuma Wurkum dake garin Makurdi babban birnin jihar ta Benue.

Rahotonnin sun ce yawancin mutanen dake zaune a unguwar Wadata sun fi kamuwa da cutar inda aka garzaya da akasarinsu zuwa asibiti.

Ana dai danganta cutar amai da gudawar da rashin tsabtacaccen ruwan sha, muhalli dama yanayin zafi, da ke haifar da asarar rayukan jama'a a dama.